AfriKDP
Securing digital asset...
Please do not close this window
Book cover
Food & Culture

Tubani Na Gargajiya Da Na Kasuwanci

A
Aminu Uzairu Tahir
Verified Creator
No reviews yet
$1.25
A cikin gidajen Hausawa, akwai wani abinci wanda ba wai kawai ciyarwa yake yi ba, face yana
ɗauke da tarihi, al'ada, da alaƙar zumunci ta tsararraki. Wannan abinci shi ne Tubani — abincin da
kakanninmu mata suka gada wa iyayenmu mata, su kuma suka gada mana, ta hanyar hannu, ba ta
littafi ba. Idan aka tuna da yadda ake tunkuɗe wake a turmi da wayewar gari, ko warin ganyen da
ake nannaɗe abinci a ciki yayin da yake tafasa a bisa wuta, sai a fahimci cewa Tubani ba sana'ar
kwanan nan ba ce — al'ada ce da ta shiga zuciyar Bahaushe.
Manufar wannan littafi ita ce ta tattara wannan gado na baka, a rubuta shi cikin tsari mai fa'ida,
domin kada al'adar shirya Tubani na asali ta ɓace a cikin sauyin zamani da yaɗuwar abincin gyaran-
gyaran da ba su da tushe a al'adarmu. A lokaci guda kuma, littafin zai nuna yadda za a iya ɗaukar
wannan sana'ar gargajiya, a inganta ta, a kuma mayar da ita hanyar samun abin dogaro da kai ba
tare da an rasa asalinta ba.
Za mu bi diddigin Tubani daga asalinsa, ta kayan da ake amfani da su — wake, gurjiya, dawa, da
rogo/alabo — har zuwa yadda ake shirya kowanne irinsa daki-daki, sannan mu kalli yadda ake
tabbatar da dandano da inganci, kafin daga bisani mu tsallaka zuwa fannin kasuwanci.
3
Secure Checkout Instant Download
Natural Food
Format
PDF Document
Language
Hausa
Pages
12 pages

Loading reviews...

A
Aminu Uzairu Tahir
Am an Educationist, Physics and Mathematics Teacher, Scientist, Islamic Researcher, Humanitarian activist and General Writer.
4
Assets Published
0
Total Sales
Your Cart